Sunday, 23 December 2018

Gwamnatin Najeriya ta maida wa Saraki martani kan kasafin 2019

Gwamnatin Najeriya ta maidawa shugaban majalisar dattijan kasar Bukola Saraki martani, kan kalamansa da ke bayyana kasafin kudin shekarar 2019 da shugaba Buhari ya gabatar a matsayin fanko, wanda ‘yan kasar ba za su mori komai daga gare shi ba.


Yayin da yake maida martanin, ministan yada labaran Najeriya Lai Muhammad, ya shaidawa manema labarai a Abuja cewa, bangaren zartarwa ba zai bata lokacinsa wajen musayar yawu da Saraki ba, kan abinda yake a bayyane ga kowa.

Ministan ya kara da cewa ba tsarin bangaren zartarwa ba ne ya rika musayar yawu da bangaren majalisa, sai dai ya jajirce wajen sauke nauyin da ya rataya a wuyansa.

Kwana guda bayan gabatar da kasafin kudin da shugaba Buhari ya yi cikin zauren majalisun kasar a ranar Laraba, Bukola Saraki ya soki kasafin na naira triliyan 8 da doriya.

A cewar shugaban majalisar dattijan, bai gamsu da bayanan shugaban Najeriya kan fayyace sahihan hanyoyin da za’a samar da kudaden aiwatar da kasafin na 2019 ba, zalika kasafin bai mayar da hankali wajen rage radadin talauci da miliyoyin ‘yan Najeriya ke ciki ba.

Saraki wanda a yanzu shi ne daraktan yakin neman zaben dan takarar jami’yyar adawa ta PDP Atiku Abubakar a zaben shugaban kasa na 2019, ya fice daga jam’iyya mai mulki ta APC a cikin wannan shekara, domin neman takarar shugaban kasa a jam'iyyar ta PDP, wadda bai yi nasara ba.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment