Sunday, 23 December 2018

Idan aka sake zaben Buhari a 2019 to kashin mu ya bushe>>Peter Obi

Mataimakin dan takarar shugaban kasa na PDP, Atiku Abubakar watau,Peter Obi ya gargadi 'yan Najeriya da cewa su guji sake zabar gwamnatin shugaba Buhari dan sake yin shekaru 4 akan mulki idan ba haka ba wahala ba ta kareba.


Peter Obin yayi wannan maganane a jihar Legas wajan wani taro da ya halarta jiya Asabat kamar yanda shafin The Cable ya ruwaito, inda yace zabar gwamnatin Buhari a karo na biyu na nuna cewa kashin 'yan Najeriya ya bushe kenan domin tattalin arzikin kasar zai ci gaba da tabarbarewane.

Obi ya bayyana cewa, la'akari da kasafin kudin shekarar 2019 da shugaba Buhari ya gabatarwa majalisa za'a iya cewa babu inda kasarnan zata je muddin Buharin ya ci gaba da mulki.

Yace kasafin kudin ya nuna cewa kashi 60 cikin dari za'a yi amfani da shine wanjan biyan bashin da ake bin kasarnan sannan kuma shi ya nuna cewa za'a tatsi talaka dan a karbi haraji, yace Najeriya fa itace kasa ta daya a Duniya a talauci to ta yaya zaga matsi wanda yake cikin talauci kace zaka karbi haraji indai ba karashi kake so ka yi ba?

Obi yace, Bafa Buharine ke gudanar da mulkin kasarnan ba kuma be damu da yanda al'amura ke gudana ba.

Yace idan aka zabesu zasu karfafawa kanana da matsakaitan masana'antu karfin gwiwa dan ganin tattalin arzikin kasarnan ya habaka

No comments:

Post a Comment