Saturday, 22 December 2018

Idan Buhari Da Gaske Ya Ke Yaki Da Cin Hanci Da Rashawa Ya Binciki Ganduje>>Naja'atu Dr. Bala

Hajiya Naja’atu Muhammad na cikin wadanda suka rika tallata Muhammadu Buhari a matsayin mafi cancanta da zama shugaban kasa a zaben 2015.


‘yar siyasar ta yi wannan jawabi ne dangane da jerin bidiyon da aka wallafa da ke zargin gwamnan Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje na karbar kudaden da aka ce cin hanci ne daga hannun ‘yan kwangila.

Ta kalubalanci gwamnatin tasu a kan rashin gudanar da bincike kan lamarin, duk da ikirarin da jami’anta ke yi da cewa suna yaki da rashawa.

“Idan zargi ne, me ya sa ba a yi bincike ba? Ai, idan ba a yi zargi ba, ba za a yi bincike ba. Idan ba a yi bincike ba, ai ba za a gano gaskiya ba.”

Ta ce a iyakar saninta, kotu ba ta isa ta hana ‘yan sanda bincike ba.
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment