Wednesday, 26 December 2018

In je Amurka in yi me?>>Atiku ya bayar da amsa yayin da aka tambayeshi ko me ya hanashi zuwa kasar Amurka

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP,Alhaji Atiku Abubakar ya bayyana cewa babu abinda zai je yayi a kasar Amurka da ake cece-kucen cewa wai ya kasa zuwa.


Atikun ya bayyana hakane a wata hira da Aliyu Mustafa Sakkwato na gidan rediyon muryar Amurka, VOA yayi dashi.

Aliyu ya tambayi Atiku cewa sun ce wai ka kasa zuwa Amurka ne dan kana tsoron kada a kamaka.

Atiku ya bayar da amsar cewa, inje Amurka in yi mene? Kuma idan na yi laifi ai a ko inama za'a iya kamani.

No comments:

Post a Comment