Thursday, 27 December 2018

Japan na neman ma'aikata daga kasashen waje

Kasar Japan na shirye-shiryen karbar ma'aikata daga kasashen waje sabili da kasancewar yawan tsofi da ya yiwa kasar yawa da ya sanya karancin ma'aikata matasa.


Akan haka, daga watan Afirilu, kasar Japan zata bude sabon tsarin bayar da visa ga wadanda keda niyyar zuwa kasarta domin gudanar da aiyukan gwamnati da na kanfunna iri daban daban.

kafar yada labaran Deutsche Welle dake yada labarai da harshen Turkanci ta rawaito cewa, kasar Japan na shirye-shiryen ingata da fadada lamurkan aiki ga baki a kasarta.

Gwamnatin kasar Japan ta dauki matakan inganta aikin ma'aikata daga kasashen waje tare da fadada tallafin ma'aikatan baki domin kara jin dadinsu a kasarta.

Daga cikin matakan da Japan din zata dauka domin inganta ma'aikata baki daga kasashen waje dake aiki a kasarta sun hada da karin albashi, rage awannin aiki a rana da kuma samar da tsarukan kare darajar aiki.

An dai kasance ana sukar kasar japan akan rashin inganta halin ma'aikata baki dake aiki a cikin kasar.

Ana dai ikirarin cewa da yawan ma'aikatan da ke zuwa kasar Japan da niyyar aiki na tsawon lokaci ko wuccin gadi suna fuskantar mu'amalar jari hujja.

Kamar yadda lawyoyi sun ka sanar, da yawan wadanda ke zuwa kasar Japan domin gudanar da aiyuka karkashin tsarin "Intern" wato koyon aiki suna gudanar da aiyuaka ne ba tare da biyansu kudin kwarai ba, kuma sukan kasance ware daga al'ummar kasar.

Bayan haka, wakilan dake taimakawa wadanan bakin ma'aikata samun aiki a Japan tun a kasashensu, su kan amshi makuddan kudade domin taimaka musu samun aikin, lamarin da kansa su cin bashi mai dinbin yawa.

Daga cikin matakan da Japan zata dauka zata magance wadanan MIYAGUN DABI'A ta hanayar yin hadaka tsakaninta da gwamnatin wadannan kasashen da ma'aikatar ke fitowa.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment