Sunday, 16 December 2018

Jaririya ta kafa tarihin warkewa daga cutar Ebola

Wata jaririya mai wata guda da rabi a duniya, ta kafa tarihin zama mafi kankantar wadda ta harbu da Ebola ta kuma warke daga cutar a Jamhuriyar Congo.

Kakakin ma’aikatar lafiyar kasar Jessica Ilunga, ta ce jaririyar mai suna Benedicte ta kamu da cutar ta Ebola ce daga mahaifiyarta, wadda ta rasu yayin haihuwarta ta, itama a dalilin kamuwa da cutar ta Ebola.

Tun daga lokacin ne aka dora jaririyar kan kulawar likitoci babu kakkautawa, kuma a cewar ma’aikatar lafiyar yanzu haka tana tare da mahaifinta da sauran iyalai.

Zuwa yanzu dai, sama da mutane 300 suka rasa rayukansu a dalilin cutar Ebola da ta sake bulla a Jamhuriyar Congo cikin watan Agustan wannan shekara.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment