Tuesday, 11 December 2018

Kalli hoton sabon jirgin Messi

Tauraron dan kwallon kafan kasar Argentina, Lionel Messi ya samu jirgin saman da zai rika yawo dashi zuwa kasashen Duniya shi da iyalanshi.


Jirgin wanda wani kamfanin jirage na kasar Argentina suka yiwa Messin sun bashi shine a matsayin kamar haya, sun kuma yi hakanne dan jawo ra'ayin manyan masu kudin Duniya dan su rika amfani da jirgin nasu wajan tafiye-tafiyensu, kamar yanda Goal ta ruwaito.

Jirgin dai na dauke da lamba goma a jelarshi watau lambar Messi ta yanda duk inda ya sauka za'a shaida cewa shine.

Sannan yana dauke da sunayen Messi dana matarshi, Antonela dana 'ya'yansu, Ciro da Mateo.


No comments:

Post a Comment