Friday, 7 December 2018

Kalli mutumin dake tabo goshinshi da harshe

Wadannan hotunan wani mutum ne me shekaru 35 me suna, Yagya Bahadur Katuwal daga yankin Urlabari dake kasar Nepal dake iya tabo goshinshi da harshenshi.Yagya dai direbane a wata makaranta sannan kuma ya watsu a kasarshi aka sanshi sosai bayan da wani abokinshi ya saka hoton bidiyonshi a shafin yanar gizo yana tabo harshenshi.

Yayi ikirarin cewa shine keda harshe mafi tsawo a Duniya sannan kuma shine mutum daya tal a Duniya dake iya tabo goshinshi da harshenshi.

Yace a lokuta da dama yara kan firgita idan suka ga ya tabo goshinshi da harshenshi yanda har fitsari a wando suke yi sannan kuma wasu manya kan suma idan suka gani.

Hukumar makarantar da yake aiki dai ta hanashi yin wannan abu a gaban yara sannan kuma ya bayyana cewa burinshi shine ya ga ya shiga kundin bajinta na Duniya.

No comments:

Post a Comment