Saturday, 1 December 2018

Karanta abinda dan Obasanjo me goyon bayan Buhari yace da aka tambayeshi tsakanin Gwamnatin Mahifinshi da ta Buhari wacce tafi?

Dan tsohon shugaban kasa, Olusegun Obasanjo me suna Olujonwo dake goyon bayan shugaban kasa, Muhammadu Buhari wanda kuma yanzu shine shugaban matasa dake goyon bayan Buhari ya bayyana cewa idan aka ce za'a hada gwamnatin mahaifinshi da ta Buhari ba'a yi adalci ba.


Ya kara da cewa dalili kuwa shine irin yana yin da mahaifinshi ya zo ya iske mulki daban dana Buhari dan haka hada su a ce wace gwamnati tafi ba adalci bane, kamar yanda Thisday ta ruwaito.

Olu ya kara da cewa, goyon bayan Buhari da yake yi ba yana nufin ya yiwa mahaifinshi rashin kunya bane, amma a matsayinshi na cikakken mutum yana da damar ya bi ra'a yinshi.


No comments:

Post a Comment