Sunday, 23 December 2018

Karanta abinda Pogba yace akan Mourinho bayan da suka lallasa Cardiff da ci 5-1

A karin farko bayan sallamar Mourinho daga horas da kungiyar Manchester United, Paul Pogba ya bayyana irin yanda yaji da kuma yanda dangantakarshi da Mourinhon ta kasance.


Pogba yayi maganane bayan da suka zazzagawa Cardiff City kwallaye 5-1 a jiya Asabar, yace, nasan kuna jiran ku ji me zance akan Jose da kuma sakamakon wasan mu na yau.

Ya kara da cewa a bayyane take cewa yau suna cikin farin ciki kuma sun yi wasa me kyau, sannan mun yi kokari sosai kuma nasan cewa kuna so ku tambayeni akan Mourinho.

Yace, a tare da Mourinho mun ci kofi kala-kala duk da cewa ba komai bane ya tafi daidai yanda ake so ba amma munci kofi kala-kala tare dashi.

Yace cin kofi yana karawa dan wasa kwazo kuma ina gode mishi da wannan.

Yace ya tabbata cewa abokan aikinshi yanzu abinda suke tunani shine wasa na gaba, Eh suna so su koma kamar da su sama sune a sama.

Abinda zance kenan, ya karkare bayaninshi.

No comments:

Post a Comment