Tuesday, 25 December 2018

Karanta amsar shugaba Buhari da aka mai tambayar cewa akwai masu juya gwamnatinshi

A wata hira da gidan redoyin VOAhausa yayi da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, wakilinta, Aliyu Mustafa Sakkwato ya tambayi shugaban dangane da wasu gungun mutane da ake kira da Cabal wanda ake rade-radin cewa suna juyashi.


Ya kara da cewa, cikin wanda suka yi wannan magana hadda uwargidanshi, A'isha Buhari, ko me zaice akan hakan?

Shugaba Buhari ya bashi amsar cewa, wannan ruwanta,  kyawun Dimokradiyya kenan da kuma irin mulkin da yake yi, kowa na da damar ya bayyana ra'ayinshi akan yanda al'amura ke gudana.

Ya kuma kalubalanci masu fadin hakan da su fadi abu da ya da aka tursasamai yayi.

No comments:

Post a Comment