Saturday, 8 December 2018

Karanta labarin fashi da makami na farko da aka taba yi a Najeriya da kuma inda aka yishi

Wannan labarin yanda fashi da makami na farko ya faru kenan a  Najeriyar yanzu da muke ciki, ya farune a shekarar 1962 a jihar Edo.

Wasu 'yan fashi da makami suka tare motar banki dake dauke da kudi suka sace Fan dubu 60 amma daga baya an kwato Fan dubu 20. Wani ma'aikaci da dan sanda sun samu rauni ba me tsanani ba. Mutane bakwai aka kama akan lamarin aka kuma tuhumesu da fashi da makami. An riga an yiwa kudin Inshora dan haka bankin dake da su ba su yi asaraba.

Bankin dama tun a baya yana biyan kudin Inshora da suka kai Fan dubu 17.5 duk shekara dan yiwa zirga-zirgar kudinshi Inshora. Amma bayan fashin sai bankin ya koma daukar asarar kudinshi da kanshi maimakon yi musu Inshora ya rika ajiye Fan dubu 15 duk shekara.
No comments:

Post a Comment