Tuesday, 25 December 2018

Karanta labarin jarumin fina-finan Indiya da har yanzu babu kamarshi

Tsoho mai ran karfe ke nan, wanda ya bar babban tarihi a fina-finan Indiya.


Dilip Kumar ya fuskanci kalubale kala-kala a rayuwarsa da farko.

Jarumin kafin ya fara fim har duniya ta san shi, ya yi gwagwarmayar neman kudi, domin kuwa har sana'ar sayar da kayan marmari ya yi.

Da ya dan tara 'yan kudadensa, sai ya je ya bude wani dan karamin shagon sayar da kayayyaki.

A haka- a haka, hat ya samu wani abokinsa wanda babban dan siyasa ne a wancan lokaci ya taimaka shi da kudi ya je domin ya shiga fim.

Ya yi sa'a kuma aka zabe shi. daga nan ne kuma al'amura suka fara canzawa.

Duk da ya ke yanzu ya tsufa sosai har ya daina fim, masana'antar fina-finai ta Bollywood ba za ta taba mantawa da irin gudunmuwar da bayar ba a lokacin da ya ke fim.

Ba a samu jarumin da har yanzu ya kama kafarsa wajen farin jini da iya fim da kuma samun lambobin yabo ba.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment