Saturday, 22 December 2018

Ko Da Ina Majalisa A Ranar Da Buhar Ya Je Ba Zan Yi Masa Ihu Ba, Saboda Na San Girman Nagaba Da Ni>>Sanata Muhammad Hassan

Sanata mai wakiltar Yobe ta Kudu a karkashin jam'iyyar PDP, Satana Muhammad Hassan ya musanta jita-jitar dake yawo cewa yana daga cikin wadanda suka yi wa shugaban kasa Muhammadu Buhari ihu a yayin da ya je gabatar da kasafin kudi a majalisa.


Sanatan ya musanta hakan ne a bayan da wasu kafafun yada labarai na bogi suka rawaito cewa bai yi da na sani kan ihun da suka yi wa shugaba Muhammad Buhari a lokacin da yake gabatar da kasafin kudin shekara ta 2019.

A yayin hirar da RARIYA ta yi da Sanatan ta wayar tarho, ya kara da cewa a ranar da Buhari ya je majalisar shi yana jihar Gombe wurin taron PDP na yankin Arewa maso Gabas da aka gudanar. Don haka ya yi mamaki yadda aka dinga yada cewa yana daga cikin wadanda suka yi wa shugaban ihu.

"Wallahi ko ina majalisa a lokacin ba zan yi wa Buhari ihu ba duk da cewa ba jam'iyyar mu daya ba, saboda na san girman na gaba da ni, musamman shugaba irin Buhari. Don haka ina mai kira ga jama'a da su yi watsi da wancan labari na bogi", inji Sanatan.
Rariya.

No comments:

Post a Comment