Saturday, 22 December 2018

Kudin da EFCC suka kama jiya namune>>Bankin Union

Hukumar gudanarwar bankin Union ta fitar da sanarwa inda tace mutanennan biyu da hukumar hana yiwa arzikin kasa zagon kasa ta EFCC ta kama jiya, Juma'a a filin jirgin saman Enugu ba 'yan dambara bane, kudin da aka kama su dasu na bankinne.


A jiyane dai ma'aikatan EFCC din suna kama mutum biyu a filin jirgin saman Enugu da kudi dalar amurka miliyan 2.8.

A sakon da Union Bank ya fitar ta dandalinshi na sada zumunta yace kai da kawon kudi tsakanin jihohin Najeriya abune da kowane banki ke yi akai-akai, kuma babban bankin Najeriya ya bayar da lasisi ga Bankers Warehouse dan yin wannan tafiye-tafiyen na kudi.

Sun kara da cewa sun yi mamakin abinda EFCC din ta yi ba tare da kammala bincike ba, wannan tafiye-tafiyen da kudi yana kan doke kuma yana daya daga cikin tsare-tsaren aikin banki.

Haka shima Bankers Warehouse dake gudanar da wannan tafiye-tafiye na kudi a madadin bankuna ya aikewa da mataimakin babban bankin Najeriya, CBN, Lawrence Ijebor da wasikar cewa ya taimaka ya saka baki akan wannan lamari saboda ma'aikatan nasu sun nunawa jami'an EFCC takardun aikinsu amma duk da haka sai da suka kama su kuma suna barazanar rike musu kudi.

No comments:

Post a Comment