Monday, 24 December 2018

Kuma dai: Atiku Abubakar ya sake yin wata karya: Matar sojan da ya ce ya kira tace be kirata ba

Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar ya sake yin wata karya da aka gano shi a karo na biyu.


A makon da ya gabatane muka ji cewa wasu 'yan Asalin garin Wurno na jihar Sakkwato sun fito sun karyata ikirarin Atikun na cewa yana da asali da garin.

Haka kuma Atiku ya bayyana ta dandalinshi na sada zumunta cewa ya kira matar sojannan da ya rasa ranshi a harin da Boko Haram suka kai Metele watau, Lt. Col. Ibrahim Sakaba inda har yace irin soyayyar da matar ke wa mijin ta ta bashi mamaki.

To saidai a rahoton Punch da tace ta yi hira da matar Sakaba me suna Seun, ta bayyana musu cewa Atiku karya yayi be kirata ba.

Tace me zai sa yayi karya haka? Ni Atiku be kirani ba.

No comments:

Post a Comment