Sunday, 23 December 2018

Kuma dai: Pogba ya sake saka hoto ya tambayi me zaku ce akanshi?

Bayan da Manchester United ta kori Jose Mourinho da ga horas da 'yan wasanta, Pogba wanda basa shiri da Mourinhon ya saka wani hoto inda yake wata irin harara dake nuna alamar kamar ya ji dadin sallamar da akawa Mourinhon inda ya tambayi mabiyanshi a shafinshi na sada zumunta cewa me zaku ce akan wannan? 


An caccaki Pogban akan wancan hoto amma daga baya ya fito ya gogeshi sannan kamfanin Adidas da Pogban kewa talla suma sun fito sun kareshi inda suka ce tallace zai musu, sa'a ce kawai aka yi abin ya zo a lokaci guda.

Pogban ya sake saka makamancin wancan hoton amma na zane da ya nunashi da ido daya a kanne inda yace to yanzu me zaku ce akan wannan hoton? Akwai wata muhimmiyar sanarwa tana nan tafe.

Ko wace irin sanarwace? Lokaci be bar komai ba.

No comments:

Post a Comment