Wednesday, 5 December 2018

Kwanannan ba da dadewa ba zan yi aure>>Nafisa Abdullahi

Tauraruwar fina-finan Hausa, Nafisa Andullahi ta bayyana cewa kwanannan bada dadewa ba in Allah ya yarda zata yi aure, Nafisar ta bayyana hakane ta dandalinta na sada zumunta.Ta saka hotunan auren Priyanka da Nick inda tace, wa ye zai yi aure nan gaba? Sai tace nice.

Ta kara da cewa, nima zan fara shiri.

Maganar gaskiya kwanannan ba da dadewa ba zan yi aure in Allah ya yarda.

Muna fatan Allah ya tabbatar da Alheri ya kuma kaimu lafiya.


No comments:

Post a Comment