Tuesday, 25 December 2018

Liverpool da City sun fi mu damar lashe kofin Premier>>Inji kocin Tottenham

Mai horar da Tottenham Mauricio Pochettino, ya ce kungiyoyin Liverpool da Manchester City na kan gaba a tsakanin takwarorinsu na Premier ta Ingila, wajen samun damar lashe kofin gasar ta bana.


Sai dai Pochettino ya ce damar da Liverpool da kuma City ke da ita fiye da su, ba zai sa su fidda ran lashe kofin gasar ta Premier ba, karo na farko tun bayan shekara ta 1961.
Kocin na Tottenham ya bayyana haka ne jim kadan bayan wasan ranar Lahadi da suka fafata, wanda suka yi tattaki har zuwa gidan Everton suka kuma lallasa ta da kwallaye 6-2.

A halin yanzu, Kungiyar Tottenham ce ta uku a teburin gasar Premier da maki 42, yayin da Manchester City ke matsayi na biyu da maki 44 sa kuma Liverpool da ke jan ragamar gasar da maki 48.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment