Monday, 3 December 2018

Luka Modric ne zai lashe kyautar Ballon d'Or

Rahotanni sun bayyana cewa, dan wasan Real Madrid, Luka Modric ne zai lashe kyautar Ballon d'Or da za'a bayar a daren yau.


Shafinnan na Marca da ya saba hakaito labarai akan wasanni kuma lokuta da dama su kasance gaskiya ne ya bayyana haka inda yace Modric ne zai kawo karshen shekaru 10 da Ronaldo da Messi suka shafe suna cinye wannan kyauta tsakaninsu.

Dan wasa na karshe da ya lashe wannan kyauta banda Ronaldo da Messi shine Kaka dan kasar Brazil a shekarar 2007 wanda kuma tuni ya rataye takalminshi ya daina buga kwallo.

Tun daga shekarar 2008 Messi da Ronaldo ne suke lashe kyautar.

Idandai wannan labari ya tabbata to Modric shima zai kafa tarihin kasancewa dan kwallon kasar Croatia na farko da ya taba lashe kyautar.

No comments:

Post a Comment