Wednesday, 26 December 2018

Mabiya Shi'a Sun Kaiwa Kiristoci Ziyarar Kirsimeti A Wani Coci Dake Kaduna

A lokacin bukukuwan Kirsimeti da Kiristoci ke gudanarwa a fadin duniya, ‘Yan Shi'a Almajiran Shaikh Ibraheem Zakzaky sun yi  amfani da wannan damar wajen kaiwa Kiristoci ziyarar a cocin ECWA GOODNEWS dake Kaduna.Shugaban Cocin Rabaran Istifanus Isa ya gabatar da wakilin 'Yan Shi'a a wurin wato Dakta Shu'aibu Musa, inda ya yi jawabi na taya murna da kuma gabatar musu da saƙon 'yan Shi'a, da kuma matsayin Kiristoci a wurin 'yan Shi'a da sauransu. Bayan nan ne, aka gabatar da waƙoƙi daga Ammar Ɗan Tinka da Muhammad Baƙir.

Mahalarta Cocin, sun nuna jin dadinsu sannan sun ce; sun ƙara fahimtar Musulunci ba addinin ta'addanci bane, addini ne na zaman lafiya. Sun kuma nuna gamsuwarsu da yadda ba a kyamace su har aka zo muhallinsu domin taya su murna.
Rariya.

No comments:

Post a Comment