Sunday, 2 December 2018

Mabiyan Rahama Sadau a Instagram sun kai miliyan 1

Tauraruwar fina-finan Hausa da turanci Rahama Sadau ta ci gaba da jan zarenta wajan zarta dukkan jaruman fina-finan Hausa maza da mata a yawan mabiya a dandalin Instagram inda a yanzu mabiyanta suka kai miliyan daya.Ko da a shafin Twitter ma Rahamar ce ke kan gaba wajan yawan mabiya a cikin jaruman masana'antar inda take da mabiya dubu dari 171 sai kuma Ali Nuhu dake biye mata baya da mabiya 165, sai kuma Hadiza Gabon da mabiya 137.

Me biwa Rahama a shafin na Instagram itace Hadiza Gabon wadda ke da mabiya da suka zarta dubu dari 888.

Sai kuma Ali Nuhu wanda shima yake da mabiya dubu dari 842, sai idan aka koma shafin Facebook Ali Nuhu yafi kowane jarumin fim din Hausa yawan mabiya kai zama a iya cewa ya nunka mabiyan dukkan jaruman fim din hausan a daidaikunsu dan yana da mabiya da yawansu ya zarta miliyan 1.6. Haka kuma da za'a hade yawan mabiyan Ali Nuhu na Facebook da Instagram da Twitter to ya zarta dukkan wani jarumi yawan mabiya a shafuka sada zumunta nesa ba kusa ba.

Me biwa Ali Nuhu a Instagram itace Fati Washa da yawan mabiyan da suka zarta dubu dari 775.

Sai kuma Adam A. Zango me yawan mabiya dubu dari  737.

Daga nan kuma sai Maryam Booth me yawan mabiyan da suka zarta dubu dari 600


No comments:

Post a Comment