Sunday, 23 December 2018

Maciji Duk Maciji Ne Kuma Kunama Duk Kunama Ce>>Naja'atu

Hajiya Naja'atu ta ce ba daidai ba ne hukumar EFCC ta juya baya a kan batun bidiyon Ganduje, don kuwa ita da 'yan sanda suna da ikon su yi bincike don tabbatarwa ko wanke zargin da ake yi.


Ta ce ita ba ta yarda ba satar da dukiyar jama'a ba, ko daga wacce jam'iyya yake.

"Maciji duk maciji ne, kowanne ne daga PDP yake ko daga APC, zai yi sara ne ya cutar da mutane. Azzalumi, azzalumi ne. Kunama ce idan za ta harbe ki, ko wacce irin tuta ta dauka, sunanta kunama. Kisa za ta yi!

Ni a ce an bar wani saboda kawai yana APC, ni wannan ban yarda da shi ba. Saboda an zalunci, zalunci ne."

No comments:

Post a Comment