Wednesday, 5 December 2018

Makauniyar Soyayya Ta Sa 'Yan Fim Sun Fi Malamai Daraja A Siyasar Nijeriya

Ina mamakin yadda wai dan fim ne zai fito yana cin zarafin malamin addini saboda ya fadi gaskiya akan gwamnati wadda aka kafa ta da siyasar da ta kunshi yaudara, karya da cin amana.

A dalilin makauniyar soyayya da ake yi wa 'yan siyasar kasar nan duk mutuncin ka sai wani mara mutunci ya ci zarafinka kuma a yaba masa. Amma idan ba haka ba, ta yaya za a fifita dan fim da malami don ya fadi gaskiya, kuma a yabi dan fim ya kare wanda aka fadi gaskiya a kansa.

Alla ha ka ganar da mu gaskiya.
Rariya.

No comments:

Post a Comment