Saturday, 1 December 2018

Makiyayan Mali ne suka shigo Sokoto>>'Yan sanda

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce mutanen da aka ce an gani a yankin jihar Sokoto, makiyaya ne daga Mali da ke shigowa duk shekara domin nema wa dabbobinsu ruwa.


Wata sanarwa da kakakin 'yan sandan DCP Jimoh Moshood ya rabawa manema labarai ya ce makiyayan sun shigo ne da matansu da yara da kuma dabbobi da suka kunshi shanu da rakuma da kuma jakuna.

Wasu rahotanni ne suka ce wata sabuwar kungiya ta masu ikirarin wa'azin Musulunci dauke da miyagun makamai, ta bulla a cikin jihar Sakoto daga jamhuriyyar Nijar mai makwabtaka da kasar.

Kuma sun soma bulla ne a wasu garuruwa na yankin karamar hukumar Tangaza inda suka kasance barazana ga al'ummar yankin.

Sai dai kuma rundunar 'yan sandan Najeriya ta ce makiyaya ne daga Mali da ke shigo wa duk shekara suna yada zango kan iyakar Najeriya domin neman ruwa.

Sannan sanarwar ta ce tun da suka shigo daga ranar Talata, ba su sake koma wa ba, kuma ba su kasance wata barazana ga wani ba, kamar yadda rahotanni suka ce suna bin kauyuka suna "karbar zakka daga masu abin hannu," kuma suna yin "bulala ga mutanen da suka aikata abubuwan assha da suka saba wa dokokin addinin Musulunci.

Rundunar 'yan sandan ta bukaci al'ummar sokoto da kewaye da su kwantar da hankalinsu, su ci gaba da gudanar da ayyukansu na yau da kullum ba tare da wata fargaba ba.Yankin Tangaza a jihar Sokoto dai na kan iyaka ne da jamhuriyar Nijar wacce ke makwabta da Mali.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment