Tuesday, 25 December 2018

Man Fetur Ya Wadata A Lokacin Kirsimeti

Bana dai Najeriya ta yi bukukuwan kirsimeti cikin walwala da wadatan man fetur, Sabanin yadda ake samun karancin man a shekarun baya.

Sashen hausa ya jiyo ra’ayoyin wasu mutane a Najeriya kan yadda aka samu wadatar man fetur a karshen wannan shekara sabanin yadda aka samu karancin man a bara.
Wadanda aka yi hira da su un bayyana cewa, babu rigimar mai kuma ana harkar kasuwa lafiya, saboda a wannan shekara an samu wadatar sa sosai, suka kuma bayyana farin cikin akan yadda aka samu wadatar man fetur a wannan lokaci na kirsimeti.
Shugaban Ma'aikatar Man Fetur ta Najeriya Maikanti Kachalla Baru, ya ce ya shigo da man fetur wadatacce, wanda har sai da ya tilastawa ‘yan kasuwa suka rika rage kudin nasu man fetur din kasa da kudin da aka kaiyade na sayar da ko wace lita daya.
Bisa ga cewar shugaban ma'aikatar man na Najeriya, akwai lita biliyan uku a kasa, sannan kuma akwai wasu a cikin jiragen ruwa da ba a riga an sauke ba, ya kara da cewa daga yanzu har zuwa bayan zaben shekara ta 2019 ba za a samu karancin mai ba.
VOAhausa.

No comments:

Post a Comment