Saturday, 15 December 2018

Manchester City sun sake hayewa saman teburin Firimiya

Kungiyar Manchester City ta sake darewa saman teburin Firmiya bayan da ta lallasa Everton da ci 3-1 a wasan da suka buga yau, Asabar.


Gabriel Jesus ne ya ci kwallaye har biyu da kuma wadda Raheem Sterling ya ci sune suka baiwa Man City Nasara inda yansu suke gaban Liverpool da maki biyu.

Dama dai masu sharhi sunce Liverpool din ba zata dade a saman Teburin ba bayan da Man City ta rikito.

Yanzu dai abin jira a gani shine ko Liverpool din zasu ci wasansu me zafi na gobe da zasu buga da Manchester United?

No comments:

Post a Comment