Sunday, 16 December 2018

Manchester United ta ji bone a Anfield, Liverpool ta koma saman teburin Firimiya

Liverpool ta sake dare kan teburin Premier, bayan da ta ci Manchester United 3-1 a wasan mako na 17 da suka kara a ranar Lahadi a Anfield.


Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Sadio Mane minti 24 da fara wasa, daga baya United ta farke ta hannun Jese Lingard minti tara tsakani, haka aka je hutu 1-1.

Bayan da aka sha ruwa ne aka koma fili, Liverpool ta kara kwallo na biyu ta hannun Xherdan Shaqiri, kuma shi ne dai ya ci na uku.

Da wannan sakamakon Liverpool ta koma ta daya a kan teburin Premier da maki 45, inda Manchester City wadda ta doke Eveton a ranar Asabar ta koma ta biyu a teburi da maki 44.

Ita kuwa Manchester United tana ta shida da maki 26 a kan teburin gasar bana.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment