Wednesday, 26 December 2018

Manchester United Za Ta Sake Neman Gareth Bale

Rahotanni sun bayyana cewa kungiyar kwallon kafa ta Manchester united ta shirya tsaf domin sake neman dan wasan kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid Gareth Bale domin ganin dan wasa yakoma ingila da buga wasa.


United dai ta dade tana neman dan wasan mai shekaru 28 a duniya wanda take ganin zai taimaka mata wajen kara karfi a gasar firmiya dana zakarun turai sakamakon kungiyar bata kokari a wanna kakar wasan wanda har korar kociyanta tayi.

Yawan jin ciwo yasa kungiyar tayi sanyi da neman dan wasan dan asalin kasar wales wanda yakoma Real Madrid daga kungiyar kwallon kafa ta Tottenham akan kudi fam miliyan 83 shekaru hudu da suka gabata.

Bale dai ya buga wasanni goma ne kawai a wannan kakar tsakanin kungiyarsa da kasarsa ta Wales sakamakon yawan jin ciwo da dan wasan yakeyi kuma dan wasan kawo yanzu yana buga wasa akai-akai a kungiyar.

Sai dai duk da yawan ciwon da dan wasan yake hakan bai hana Manchester United sake neman dan wasan ba inda ta shirya tsaf domin komawa don nemansa a kakar wasa mai zuwa.

Real Madrid dai tayiwa dan wasan kudi fam miliyan 85 a kwanakin baya sai dai a ‘yan kwanakin nan rahotanni sun bayyana cewa Madrid din ta rage farashin dan wasan zuwa fam miliyan 62 domin a samu mai siya.

A kakar wasan data gabata dai dan wasan ya zura kwallaye 12 ne kawai cikin wasanni 32 daya buga gaba daya daga Real Madrid har kasar sa ta Wales sai dai ya taiamkawa kungiyar ta lashe kofin zakarun turai da suka doke Liberpool da ci 3-1.
Leadershipayau.

No comments:

Post a Comment