Sunday, 2 December 2018

Me horas da Liverpool yayi kutse a filin dan murnar kwallon da suka ci

Me horas da 'yan wasan kungiyar Liverpool, Jurgen Klopp ya kasa boye murnarshi bayan da dan wasanshi, Divock Origi ya saka kwallo a ragar Everton ana gaf da tashi cikin minti 96 yayin da kowane cikin kingiyoyin ke neman kwallo ido rufe.


Cin kwallon Origi ke da wuya Klopp ya tashi ya dankara da gudu cikin fili ya rungume me tsaron gida na kungiyar tashi, Allison yana jefa hannaye sama dan murna. Sai daga bayane sannan yaje yayi murnar tare da sauran masu taimaka mishi na wajan fili.

Wasan dai ya kare da Liverpool din na cin Everton 1-0.

Bayan kammlaa wasan Klopp ya bayyanawa Sky Sport cewa, be yi niyyar nuna rashin da'a ba amma abin ya zomai ne cikin murna kuma ya kasa rike murnar shi yasa ya shiga filin da gudu.

Yace ba da gangan bane amma yana jiran hukuncin da hukumar kula da kwallon zata dauka akan wannan abu da yayi.

No comments:

Post a Comment