Sunday, 16 December 2018

Me yasa 'yan fim basu auren 'yansanda?>>Ku tayani addu'a na kamu da soyayar Maryam Yahaya

Soyayya gamon jini kuma soyayya takan shiga zuciyar mutum ba tare da ya ankara ba, abinda ya faru da wani jami'in dan sanda kenan me suna Rilwanu Bala inda yace shi yanzu duk Duniyarnan babu wacce yake son aure kamar tauraruwar fina-finan Hausa, Maryam Yahaya.


Rilwanu yayi tambayar cewa wai me yasa 'yan fim basa auren 'yan sanda domin shi ko a tarihi be taba jin wata 'yar fim tana soyayya dan sanda ba amma shi gashi yanzu ya kamu da soyayyar Maryam Yahaya duk da cewa sau daya ya taba ganinta.

Gadai abinda ya rubuta a shafinshi na Facebook:

'Meyesa Yan Fina Finai Hausa Film Basa Son Aure Yan Sanda?

Koh ga Tarihi banta bajin ance wata Yar Film Hausa Tana Soyayya Da Wani Dan Sanda A Nigeria ba,

Balaima Haar ace ta Aure shi 
Gashi kuma ina matukar Son Yar Film Hausa Maryam Yahaya Kuma 

Wallahi Ina Son In Aureta duk Da Cewa sau Daya Na Taba Haduwa Da Ita Amma GsKia ina Qaunarta,

Dan allah Friends Kubani Shawara Tayaya sakona zai isa wurinta'

Rilwani ya kara da cewa, Kusani Cikin Addu,ar ku Friends Saboda Nariga Najijita 
Kuma na Fada Tarkon Soyayyar Maryam Yahaya.

Da abin yayi kamari, Rilwanu ya saka wannan hoton na kasa inda yake dauke jaka yace ya shirya tsaf dan zuwa Kano neman neman auren Maryam.

Ga abinda yace:
JIJITAR S0
KUBANI SHAWRA

Yau Zanje Kano Wajan Neman Aure Maryam Yahaya,

A Ina Yakamata Nafara
 Wajan Ali Ali Nuhu
Wajan Iyayyen Maryam,
Wajan Ita Kanta Maryam Yahaya,

Dan Allah Kuyi Share Saboda Naji Shawar Mutane. arziki dan wallahi Ina Qaunar Maryam Yahaya ,

No comments:

Post a Comment