Sunday, 2 December 2018

Membobin APC Su 820 Sun Sauya Sheka Zuwa PDP A Jihar Sokoto

Gwamnan jihar Sokoto Rt. Hon. Aminu Waziri Tambuwal CFR (Mutawallen Sokoto) ya shaidi sauya shekar Mutum Dari Takwas da ashirin 820 'Ya'yan Jam'iyar APC zuwa Jam'iyar PDP, a karamar Hukumar Wuron wato yankin da Shugaban Jam'iyar APC na Jahar Sokoto ya fito.Mataimakin Gwamnan jihar Sokoto Hon. Dr. Manir Dan Iya (Sardaunan Kware), Tsohon Mataimakin Gwamna Sokoto Barr. Mukhtar Shehu Shagari, Shugaban Jam'iyar PDP na jaha Alh. Ibrahim Milgoma, tare da sauran Mukarraban Gwamnatin Jahar Sokoto ne, tare da sauran magoya baya ne suka samu halartar wannan taron.

An yi taron ne a hedikwatar PDP ta karamar Hukumar Mulkin Wurno, a karamar Hukumar Mulkin Wurno, cikin kwanciyar hankali.
Rariya.

No comments:

Post a Comment