Saturday, 8 December 2018

Ministar Kudi Ta Jagoranci Zama Don Kirkiro Da Sabuwar Hanyar Samun Kudin Shiga Ga Nijeriya

A kokarin da Nijeriya ke yi na kirkiro da wasu hanyoyi da ba na man fetir ba don samun karin kudaden shiga, Ministar Kudi Zainab Shamsuna Ahmad a yau ta gana da jami'an kamfanin 'African Natural Resources and Mines Limited', wanda Mr. Raji Gupta ya jagoranta, don zuba jarin Dala Miliyan Dubu Dari Shida ($600m) a harkar tono ma'adanai da karafa a karamar Hukumar Kagarko dake Jihar Kaduna. 


Kimanin shekara ashirin kenan rabon da a samu yarjejeniyar zuba jari irin wannan mai girma a fannin ma'adanai. Za'a dinga samar da ton miliyan biyar da dubu dari hudu (5.4m) na ma'adanai a kowace shekara; sannan aikin zai samar da aikin yi ga dubun-dubatar 'yan Nigeria.

Bangaren samar da karafa na aikin zai maida hankali ne akan tono tama da karafa, tare da sarrafasu zuwa nau'in karfen da aka fi bukata wajen kere-kere. 

Har ila yau, aikin zai samar da wutar lantarki mai karfin megawatt 36 wanda hakan zai taimaka wajen inganta wutar lantarki a karamar Hukumar Kagarko don bunkasa masana'antu tare da kawo cigaba a yankin. Sannan za a karkatar da rarar wutar da aka samu zuwa Rumbun Samar da Lantarki na Tarayya don amfanar kasa baki daya. 

Ko shakka babu, wannan aiki ne da zai bunkasa masana'antu da kawo cigaba da samar wa jama'a aikin yi da rage shigo da kaya daga waje da kawo ci gaban tono karafa wanda hakan zai kawo alheri ga yankin tare da bunkasa bangaren  tono ma'adanai.
Rariya.

No comments:

Post a Comment