Saturday, 15 December 2018

Muhawarar 'yan takarar mataimakan shugaban kasa: Karanta maganganun da Osinbajo da Peter Obi suka yi da suka dauki hankula

A jiyane 'yan takarar mataimakan shugaban kasa a zabe me zuwa suka yi muhawara akan irin muradun da jam'iyyunsu ke karewa da kuma tsare-tsaren da suke da shirin yi idan an zabe su.


Mataimakin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo na daya daga cikin wadanda aka yi wannan mahawara dasu kuma akwai wata magana da ya fada a gurin mahawarar da ta dauki hankulan mutane sosai.

Maganar kuwa itace, Idan aka bari mutane suka sace abubuwan shago to lallai babu shago kenan.

Shi kuwa Peter Obi, mataimakin Atiku sai cewa yayi ba zaka bar shagon kaba ka tafi kana bin barayin kayan shago ba.

Haka kuma maganar da Peter Obi yayi na mayar da Najeriya kamar kasar kasar China ita ma ta dauki hankulan mutane inda da dama a shafukan sada zumunta suka bayyana cewa su fa a China kashe barayin shuwagabanni suka yi

No comments:

Post a Comment