Thursday, 6 December 2018

Mulki ba sauki ji nike kamar in tsere>Gwamna El-Rufai

Gwamnan jihar Kaduna Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa idan ya fadi zabe me zuwa cikin ruwan sanyi zai sauka daga mulki.


Gwamnan ya bayyana hakane a wajan  taro kan zabe da kungiyar kula da zaman lafiya ta shirya a jihar Kaduna, gwamnan ya kara da cewa a matsayinshi na dan takarar APC idan ya fadi zabe zai sauka daga mulki. Saidai yace yana son gayawa masu son zama gwamna cewa aikin gwamna ba aiki ne me sauki ba, shima ji yake kamar ya tsere.

Gwamnan ya sha alwashin daukar matakan da suka dace akan duk wanda yake kalaman kiyayya da na har zuka mutane ta fannin addini a jihar ta Kaduna.

Gwamnan ya kara da cewa ya kamata ace yana tare da iyalinshi a mafi yawan lokuta amma be samu damar yin hakan ba cikin shekaru 10 da suka gabata, kamar yanda Dailypost ta ruwaiyo.

No comments:

Post a Comment