Sunday, 2 December 2018

Nazir M. Ahmad ya zama sarkin wakar Sarkin Kano

Mai martaba sarkin Kano Muhammadu Sanusi na II ya nada Nazir M. Ahmad a matsayin sarkin wakarsa.


Danburan Kano ne ya tabbatar wa Nazir da wannan sarautar a cikin wata takarda daga fadar sarki Sanusi, kamar yadda Aminu Saira yayan Nazir ya tabbatar wa BBC.

Aminu Saira ya ce takardar na kunshe ne da sakon godiya ga Nazir da kuma tabbatar ma sa da sarautar Sarkin wakar Sarkin Kano.

"Mai martaba ya umurce ni da na yi maka godiya bisa biyayya da soyayya da kake masa tun yana Dan Majen Kano har Allah ya sa ya zama Sarkin Kano wannan abin a yaba maka ne," in ji Danburan a cikin takardar.

Ya kara da cewa. "bisa haka mai martaba ya umurce ni da na sanar da kai cewa ya ba ka sarautar sarkin wakar sarkin Kano.

Sanarwar ta kara da cewa za a yi nadin sarautar ne a ranar Alhamis 27 ga watan disamba a fadar mai martaba sarkin Kano.

Ana ganin dai wannan sabuwar sarauta ce da a ta taba yi ba a masarautar Kano, inda Sarki ne ya ga ya dace a kirkiro da sarautar kuma a ba Nazir M. Ahmad.

Nazir M. Ahmad ya rera wa Sarkin Kano wakoki da dama, kuma an dade ana kiransa da Sarkin waka tun kafin tabbatar da wannan sarautar daga Sarkin Kano saboda basira da baiwar waka da Allah Ya ba shi.
BBChausa.

No comments:

Post a Comment