Wednesday, 26 December 2018

Neymar nason komawa Barcelona

Dan wasan gaba na kasar Brazil mai taka leda a kungiyar kwallon kafa ta PSG, Neymar ya Qagu ya dawo tsohuwar kungiyarsa ta Barcelona, kamar yadda rahotanni suka tabbatar.


Dan wasan yabar kungiyar ne zuwa kungiyar kwallon kafa ta Paris-Saint German dake Faransa, kan zunzurutun kudin da ba a taba sayen dan wasa ba yuro miliyan €222.

Sai dai wasu rahotanni suna nuni da cewar dan wasan na son komawa Spaniya, don cigaba da taka leda a tsohowar kungiyarsa da ya barta shekaru biyu baya.

A baya anyi ta alakanta dan wasan da komawa kungiyar, da itace babbar abokiyar hamayyar Barcelona, wato kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, don maye gurbin Cristino Ronaldo, wanda ya hade da tawagar kungiyar Juvestus na kasar Italiya a farkon wannan kakar wasa ta bana.
Dandalinvoa

No comments:

Post a Comment