Tuesday, 25 December 2018

Nura Hussain ya musanta aika Mahaifinshi ya baiwa Dr. Ahmad Gumi Hakuri

A yayin da ake tsammanin lamarin da ya wakana tsakanin tauraron fina-finan Hausa, Nura Hussain da shehin malamin addinin Islama, Sheikh Dr. Ahmad Gumi yazo karshe bayan da rahotanni suka nuna cewa, Nuran ya aika mahaifinshi gurin Dr. Gumi akan ya yafe mishi abinda ya mishi, to Nuran dai ya musanta wancan aike.


A wani bidiyo da shugaban hukumar tace fina-finai ta Kano, Isma'il Na'abba Afakallahu ya wallafa a dandalinshi na sada zumunta, an jiyo Nura na cewa yaji rade-radin cewa Nura Hussain ya aika mahaifinshi ya baiwa Dr. Ahmad hakuri akan zagin da ya mishi, saidai Nura yace yayi tsammanin wani Nuranne daban amma sai yaji ana cewa Nura Hussain dan fim, to a nanne yasan da shi ake.

Yace shi bai zagi Dr. Ahmad Gumi ba, abinda yace shine, la'anar da Gumin yayi akan sake zaben Shugaban kasa, Muhammadu Buhari itace yace bata kamata ba. Kuma babu wani addinin da ya yadda da haka.

Ya kara da cewa, Musulunci addinine da ke cike da adalci wanda masu bautar gumaka ma ba'a yadda ka zagesu ba dan kada su ma su zagi Allah, abu na biyu dana ce shine, Qul'ya ta raba gaddama tsakanin musulmi da wanda ba musulmi ba, ballantana babancin akida ko kuma jam'iyyar siyasa, ka yi naka in yi nawa.

Nura ya kara da cewa, Soyayyar Buhari abune da suka sawa kansu wanda kuma babu ranar dainawa, kuma sun duba cancanta da girma wajan yin wannan zabi.

Ya kara da cewa su yin Buhari da fa suke yi sun san cewa yana sonsu kamar yadda yake son kasarnan su kuma sun san cewa sun fi son kansu da su, ya kara da cewa addu'arsu itace Allah ya karo mana irin Buhari.

No comments:

Post a Comment