Sunday, 16 December 2018

Pogba da Mourinho zasu bar Man United

Rahotanni sun bayyana cewa, tauraron dan kwallon Manchester United, Paul Pogba zai bar kungiyar a watan Janairu zuwa kungiyar Juventus a matsayin musanya.


Jaridar Mirror ta bayyana cewa Juve zata bayar da Miralem Pjanic ko Alex Sandro a matsayin musanyar Pogba.

Dama dai an jima ana samun sabani tsakanin Pogba da Me horas da kungiyar, Jose Mourinho.

Shima Mourinhon a wani rahoton jaridar Express ta bayyana cewa kungiyar Inter Milan na zawarcinshi.

Me horas da kungiyar ta Inter, Luciano Spalletti kwantirakin aikinshi zai kare nan da karshen kakar wasan bana kuma babu tabbacin ko Inter zata sake rikeshi.

No comments:

Post a Comment