Tuesday, 4 December 2018

Ramos ya buga wa Real La Liga 405

Kyaftin din Real Madrid, Sergio Ramos ya zama daya daga 'yan kungiyar da suka buga mata wasannin La Ligar Spaniya da yawa a tarihi.


Real ta doke Valencia a Santiago Bernabeu a gasar La Liga da ci 2-0 a ranar Asabar, kuma shi ne wasa na 405 da Ramos ya yi, hakan ya sa ya dara Michel wanda ya yi 404 tsakanin 1981-1996 a Madrid.

Ramos ya fara buga wa Madrid wasa ranar 10 ga watan Satumbar 2005 a Santiago Bernabeu a karawar da ta yi da Celta Vigo.

Cikin wasa 405 da ya buga a La Liga an ci karawa 272 da shi ya kuma ci kwallo 57 a raga, tuni ya kuma ci hudu a kakar 2018/19, sannan ya lashe kofin La Liga hudu a Real Madrid.
Ramos na shirin doke tarihin da Camacho ya kafa na buga wa Real wasa 414, jumulla Raul ne kan gaba da ya yi wa Madrid wasa 550 daga tsakanin 1994-2010
BBChausa.

No comments:

Post a Comment