Sunday, 23 December 2018

Rashin abinci da kuma kudin sayen biskit a gidan mu suka sa na dage dan zama shahararren dan kwallo>>Neymar

Tauraron dan kwallon kasar Brazil, Neymar wanda ke bugawa kungiyar PSG wasa ya bayyana irin yanda ya taso cikin rashin kudi ta yanda ko kudin sayen isasshen biskit baya iya samu a matsayin karamin yaro.


Neymar ya bayyana hakane a wata hira da yayi da wani shafin Youtube me suna, O Primo Rico, yace ya taso da son cin biskit a lokacin yana yaro inda ya bayar da labarin cewa akwai wata rana da ya tambayi mahifiyarshi yana so ya ci biskit sai ta ce mai basu da kudi ya jira sai an biya mahaifinshi albashi zata sai mishi.

A nan ne sai Neymar din ya ce mata shi kuwa yayi alkawarin nan gaba sai ya sayi kamfanin yin biskit ta yanda zai ci yanda yake so yayi hani'an.

Neymar yace mahaifiyarshi a duk lokacin da take bayar da wannan labari saboda shauki sai ta zubar da hawaye.

Ya kuma ce irin wadannan abubuwa da suka faru a rayuwarshine yasa ya dage dan ganin ya zama tauraron dan kwallo ya kuma samu kudi masu yawa.

Neymar dai ya zama dan kwallon da ya fi kowane tsada bayan da kungiyar Barcelona ta sayar dashi zuwa PSG a kudi kusan Fan miliyan dari 200.

No comments:

Post a Comment