Saturday, 1 December 2018

Rashin aikin yi na kara ta'azzara a Italiya

Bayan watan Satumba, rashin aikin yi ya kara daduwa sosai a watan Oktoba.


Hukumar Kididdiga ta Italiya ta fitar da alkaluman cewa, a watan Oktoba kaso 10.6 na jama'ar kasar ne ba su da aikin yi. Adadin mutanen da aka yi wa rejista da ba su da aikin yi a kasar sun kai miliyan 2 da 746 wanda ya dadu sama da watan Satum da adadin mutane dubu 64.

A tsakanin matasa kuma rashin aikin ya karu da kaso 0.1 a watan Oktoda idan aka kwatanta da watan Satumba wanda ya kama kaso 32.5.

Idan aka kwatanta wadannan alkaluma da na shekarar 2017 a irin wannan lokaci za a ga ya ja baya. A watan Oktoban 2017 kaso 11.1 na jama'ar Italiya ne ba su da aikin yi.
TRThausa.

No comments:

Post a Comment