Monday, 3 December 2018

Ronaldo da Griezmann ba za su je wajan bayar da kyautar Ballon d'Or ba

Wani ma'aikacin shahararren kafar watsa labarannan ta Sky Sport, Alessandro Alciato yayi ikirarin cewa, tauraron dan kwallon kafar Juventus, Cristiano Ronaldo ba zai halarci gurin bayar da kyautar Ballon d'Or da za'a yi a daren yau ba.


Haka kuma ya kara da cewa, shima dan wasan Atletico Madrid, Watau Antoine Griezmann bazai halarci gurin bayar da kyautar ba da za'a yi yau a birnin Paris na kasar Faransa ba.

Ya kuma kara da cewa, Modric ne ya zo na daya a bayar da kyautar sai Ronaldon yana biye mishi a matsayin na biyu.

Ya kara da cewa, Kylian Mbappe ne zai lashe kyautar Ballon d'Or ta matasa 'yan kasa da shekaru 21.

No comments:

Post a Comment