Saturday, 15 December 2018

Ronaldo da Messi kansu kawai suka sani>>Modric

Tauraron dan kwallon Real Madrid, Luka Modric ya soki Cristiano Ronaldo da Lionel Messi bisa rashin halartar gurin bashi kyautar gwarzon dan kwallon Ballon d'Or da aka yi a Faransa.


Modric yace hakan na nuna cewa Ronaldo da Messi kawunan su kawai suka sani kuma basu daraja sauran mutanen da suka shafe shekaru 10 suna zabarsu ba a matsayin gwamayen gasa, da 'yan kallo da sauran abokan sana'arauba.

Modric ya kara da cewa, amma ba zai iya fadin dalilin da yasa wani be halarci wajan bayar da kyautarba

Modric ya kara da cewa, lashe gasar Ballon d'Or ba yana nufin dan wasa yafi kowa bane, yana nufinne a wannan shekarar shine gwani, kamar yanda ya gayawa Sportske Novosti.

No comments:

Post a Comment