Sunday, 2 December 2018

Ronaldo ya kafa tarihin da rabon da aga irin shi tun shekaru 60 da suka gabata

Tauraron dan kwallon kasar Portugal me bugawa kungiyar Juventus wasa, Cristiano Ronaldo ya sake kafa tarihin da rabon da aga irinshi tun shekaru 60 da suka gaba a kungiyar bayan da ya saka kwallo a wasansu na jiya da Fiorentina.


An tashi wasan dai Juve na cin Fiorentina 3-0 wadda harda kwallon da Ronaldo yaci, hakan ya kaiga yawan kwallayen shi 10 kenan a cikin wasanni 14 na gasar Serie A da ya buga a kakar wasanshi ta farko a kungiyar, dan wasan da ya taba kafa irin wannan tarihin shine John Charles a kakar wasan shekarar 1957/58.

A jawabin bayan wasan da me horas da 'yan wasan kungiyar ta Juve, Allegri yawa manema  labarai ya fada cikin barkwanci cewa Ronaldo ya cisu kwallo da bugun daga kai sai me tsaron gida a baya kuma kamin a yafemai wancan cin da ya musu to dole ya tabbatar yana cin duk bugun daga kai sai me tsaron gida da zaiwa Juven.

Haka kuma a wasan na jiya, a karin farko an canja Ronaldon ana tsaka da wasa, bayan da ya ciwa  Juven kwallon ta Uku an baiwa Ronaldo katin gargadi saboda buga kwallo da yayi wanda hakan yasa Allegri ya canjashi.
No comments:

Post a Comment