Tuesday, 25 December 2018

Ronaldo ya sa gidansa a kasuwa

Cristiano Ronaldo na Juventus ya sa katafaren gidansa da ke birnin Manchester a kasuwa, matakin da bai yi wa magoya bayan Manchester United da dama dadi ba, wadanda ke sa ran dan wasan zai iya dawowa kungiyar wani lokaci nan gaba.


A shekarar 2006, Ronaldo ya sayi gida a yankin Cheshire lokacin da tauraruwarsa ke haskawa a kungiyar Manchester United, karkashin jagorancin kocinta Sir Alex Ferguson.

A waccan lokacin dai Ronaldo ya sayi gidan ne kan fam miliyan 3 da dubu 85.

Yunkurin dai ba shi ne karo na farko da Ronaldo ya yi ba wajen saida gidan nasa, domin a shekarar 2009, lokacin da ya koma Real Madrid, ya sanya shi a kasuwa amma hakarsa ba ta cimma ruwa ba.

Kafin komawar Ronaldo Juventus daga Real Madrid, wasu kafafofin yada labarai sun sha rawaito cewa akwai yiwuwar tsohon gwarzon dan wasan na duniya ya koma tsohuwar kungiyarsa ta United domin kammala kwallonsa.
RFIhausa.

No comments:

Post a Comment