Monday, 3 December 2018

Ruwa ba sa'an kwando bane: Zamu yi rugu-rugu da hancin Atiku a zaben 2019>>Dambazau

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau ya bayyana cewa, shugaban kasa,Muhammadu Buharine kawai dan takara a zaben 2019 inda yace Atiku kwata-kwata ba sa'an Buhari bane.


Dambazau ya bayyana hakane a sakatariyar jam'iyyar APC a Babban birnin tarayya, Abuja, kamar yanda Punch ta ruwaito, ya kara da cewa, shi, Atiku dake cewa wannanne zabe mafi zafi da za'a sha gumurzu to a gurinshi kenan amma ba a gurin shugaba Buhari ba da APC, a gurin Buhari wannanne zabe mafi sauki.

Ya kara da cewa ko Adamawa Atiku ba zai ci ba kuma zasu tabbar da cewa wannanne karin karshe da Atikun zai fito takara dan zasu tabbatar sunyi rugu-rugu da hancinshi sai yayi jini.

No comments:

Post a Comment