Saturday, 8 December 2018

Salah ya ci kwallaye 3 amma yaki karbar kyautar gwarzon dan wasa ya kuma kafa tarihi

A wasan Firmiya da aka buga yau, Liverpool ta lallasa Bournemouth da ci 4-0 wanda Mohamed Salah ya ci kwallaye 3.


Wadannan kwallaye da Salah ya ciwa Liverpool sun bashi damar zama dan wasan da yafi cin yawan kwallaye a kakar bana.

Saidai bayan kammala wasan an baiwa Salah kyautar gwarzon dan wasan da aka buga amma yace bazai karba ba, ya baiwa James Milner kyautar dan taya shi murnar buga wasannin Firimiya 500. Salah yace yana tayashi murnar wannan nasara da ya samu sannan kuma bazai amshi kyautar ta gwarzon wasan ba saboda Milner dinne ya cancanci amsarta

Shima Milner ya yaba da wannan halin dattako da Salah din ya nuna.

Har ila yau kwallayen da Salah din yaci a yau tasa ya shafe tarihin da Fernando Torres ya kafa inda yanzu Salah dinne ya zama dan wasan Liverpool da ya ci kwallaye 40 cikin wasannin da basu wuce 52 da ya buga.

Yanzu dai Liverpool ta hau saman teburin Firimiya da maki 42 inda Man City ta dawo ta biyu da maki 41 haka kuma a gaba dayan turai yanzu Messi ne kadai ke gaban Salah din da kwlallaye 43 yayin da shi kuma yake da 42.

No comments:

Post a Comment