Monday, 3 December 2018

Shugaba Buhari ya halarci bude taron canjin yanayi a Poland

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari a yau, Litinin ya halarci bude taro kan dumamar yanayi da aka fara yi a birnin Katowice na kasar Poland, shugaban ya hadu tare da tattaunawar diflomasiyya da shuwagabannin wasu kasashen Duniya a gurin taron.


Daga cikin wadanda shugaban ya gana dasu akwai ministan muhalli na kasar ta Poland da kuma magajin garin birnin Katowice.

Haka kuma ya gana da firaministan Netherlands, Mark Rutte a gurin taron.

Shugaba Buhari ya kuma gana da shugabar bankin Duniya Kiristalina Georgieva.

Haka kuma shugaban ya gana da shugaban kasar Austria, Alexander Van der Bellen.

No comments:

Post a Comment