Tuesday, 25 December 2018

SON ZUCIYAR BUHARI NA TSORATA NI

1. A ranar maulidi da Milyoyin Musulmi suka raja'a wajen kira da a yi koyi da Annabi SAW. Tshon nan ya yi kira gare mu da muyi koyi da halayen Jonathan saboda Maulidin Annabi SAW yayi arba da ranar Maulidin Jonathan wanda ya ba shi mulki.


2. Daren jiya da Musulmin Arewa suka kwana cikin zullumin halin da yan uwansu na Zamfara ke ciki, Baba ya kwana a fadarsa yana rera baitukan maulidi Yesu Almasihu shi da shugaban Jam'iyya da Na'ibinsa suna bukukuwan kirsimeti .

Ban ce kada Baba ya yi wa kiristoci Barka da kirsimeti ba, amma 

1. idan maulidi bidi'a ce gareshi menene matsayin kirsimeti kuma?

2. Me yasa ya fi muhimmanta koyi da Jonathan kan Annabi Sallallahu Alaihi Wa Sallam? 

3. Me ya sa ya fi muhimmanta wakewaken biki kan Halinda Zamfarawa ke ciki? 

Duk saboda son wa kansa kujerar Mulki?
Daga Rahma Abdulmajid 
Sarauniya.

No comments:

Post a Comment